Acts 20

Bulus Ya Ratsa Makidoniya da Giris

1Saʼad da hayaniyar ta kwanta, sai Bulus ya aika a kira almajiran, kuma bayan ya ƙarfafa su, sai ya yi bankwana ya tafi Makidoniya. 2Ya ratsa wurin yana ƙarfafa mutanen da kalmomi masu yawa, a ƙarshe kuma ya kai Giris, 3inda ya zauna wata uku. Da yake Yahudawa sun ƙulla masa makirci, a lokacin da yake shirin tashi cikin jirgin ruwa zuwa Suriya, sai ya yanka shawara yǎ koma ta Makidoniya. 4Sai Sofater ɗan Farrus daga Bereya, Aristarkus da Sekundus daga Tassalonika, Gayus daga Derbe, Timoti ma, da Tikikus da Turofimus daga lardin Asiya suka tafi tare da shi. 5Waɗannan mutane suka sha gaba suka kuma jira mu a Toruwas. 6Amma muka tashi daga Filibbi a jirgin ruwa bayan Bikin Burodi Marar Yisti bayan kuma kwana biyar muka sadu da sauran a Toruwas, inda muka zauna kwana bakwai.

Ta da Yutikus daga Matattu a Toruwas

7A ranar farko ta mako muka taru wuri ɗaya don gutsuttsura burodi. Bulus ya yi wa mutane magana, don yana niyyar tashi washegari, sai ya yi ta yin magana har tsakar dare. 8Akwai fitilu da yawa a ɗakin gidan saman da muka taru. 9Akwai wani saurayi zaune a taga mai suna Yitikus, wanda barci mai nauyi ya ɗauke shi yayinda Bulus yake ta tsawaita magana. Saʼad da yake barci, sai ya fāɗi daga gidan sama a hawa ta uku aka kuma ɗauke shi matacce. 10Sai Bulus ya sauka, ya miƙe a kan saurayin ya rungume shi, ya ce, “Kada ku damu, yana da rai!” 11Sai ya koma ɗakin da yake a gidan sama, ya gutsuttsura burodi ya kuma ci. Bayan ya yi magana har gari ya waye, sai ya tafi. 12Mutanen suka ɗauki saurayin da rai zuwa gida suka kuma taʼazantu ƙwarai da gaske.

Bankwanan Bulus ga Dattawan Afisa

13Mu kuwa muka ci gaba zuwa jirgin ruwan muka tashi muka nufi Assos inda za mu ɗauki Bulus. Ya yi wannan shirin don zai tafi can da ƙafa. 14Da ya same mu a Assos, sai muka ɗauke shi a jirgin ruwan muka zo Mitilen. 15Washegari muka tashi cikin jirgin ruwa daga can muka zo gefen Kiyos. Kwana ɗaya bayan wannan, sai muka ƙetare zuwa Samos, washegari kuma muka iso Miletus. 16Bulus ya yanke shawara ya wuce Afisa a jirgin ruwa don kada yǎ ɓata lokaci a lardin Asiya, gama yana sauri ya kai Urushalima, in ya yiwu ma, a ranar Fentikos.

17Daga Miletus, Bulus ya aika zuwa Afisa a kira dattawan ikkilisiya. 18Da suka iso, sai ya ce musu: “Kun san irin zaman da na yi tun lokacin da na zauna da ku, daga ranar farkon da na zo cikin lardin Asiya. 19Na bauta wa Ubangiji da matuƙar tawaliʼu har da hawaye, da gwagwarmaya iri irin da na sha game da makircin Yahudawa. 20Kun san cewa ban yi wata-wata yin muku waʼazi game da duk abin da zai amfane ku ba amma na koyar da ku a fili da kuma gida-gida. 21Na yi shela ga Yahudawa da Helenawa cewa dole juye ga Allah cikin tuba su kuma amince da Ubangijinmu Yesu.

22“Yanzu kuma Ruhu ya tilasta ni, za ni Urushalima, ba tare da sanin abin da zai faru da ni a can ba. 23Na dai san cewa a kowane birni Ruhu Mai Tsarki yakan gargaɗe ni cewa kurkuku da shan wuya suna jirana. 24Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni-aikin shaida bisharar alherin Allah.

25“Yanzu na san cewa ba ko ɗaya daga cikinku wanda na zazzaga ina muku waʼazin mulkin Allah da zai sāke ganina. 26Saboda haka, ina muku shela a yau cewa ba ni da alhakin kowa a kaina. 27Gama ban yi wata-wata a sanar muku dukan nufin Allah ba. 28Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa. 29Na san cewa bayan na tafi, mugayen kyarketai za su shigo cikinku ba za su kuwa ƙyale garken ba. 30Ko cikinku ma mutane za su taso su karkatar da gaskiya don su jawo wa kansu almajirai. 31Saboda haka ku zauna a faɗake! Ku tuna cewa shekara uku, dare da rana ban taɓa fasa yin wa kowannenku gargaɗi ba, har da hawaye.

32“To, yanzu na danƙa ku ga Allah da kuma ga maganar alherinsa, wadda za ta iya gina ku ta kuma ba ku gādo a cikin dukan waɗanda aka tsarkake. 33Ban yi ƙyashin azurfa ko zinariya ko tufafin kowa ba. 34Ku kanku kun san cewa hannuwan nan nawa sun biya mini bukatuna da kuma na abokan aikina. 35Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tukuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce: ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”

36Da ya faɗi haka, ya durƙusa tare da dukansu ya yi adduʼa. 37Sai dukansu suka yi kuka suka rungume shi, suka kuma yi masa sumba. 38Abin da ya fi sa su baƙin ciki shi ne maganarsa da ya ce, ba za su ƙara ganin fuskarsa ba. Sai suka raka shi zuwa wajen jirgin ruwa.

Copyright information for HauSRK